Wasu ma’aurata da suka kwashe shekara goma sha uku a tare sun bayyana cewa ƴan’uwan juna ne na jini.
Ma’auratan waɗanda ƴan ƙasar Amurka me sun bayyana wannan lamarin mai matuƙar taɓa zuciya nr a wani bidiyo da @stzyathletemo ya sanya a manhajar TikTok. Tuni bidiyon na su har ya bazu. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA: Yadda wani matashi ya haɗa mota da sanduna, bidiyon ya ɗauki hankula
Mijin wanda yayi magana a madadin iyalan, ya bayyana cewa sun yi aure ne a shekarar 2008 sannan suka haifi ɗan su na farko a shekarar 2011.
A shekarar 2015, mijin ya bayyana cewa sun haifi ɗan su na biyu sannan sun kwashe shekara 13 suna rayuwa tare. Sai dai, basu daɗe da gano cewa ashe su ƴan’uwa ne na jini ba.
Wannan labarin na su dai ya taɓa zuciyar mutane da dama inda suka yi ta yin sharhi akan sa.
Ga kaɗan daga ciki:
kevinellis211 ya rubuta:
Hakan yana faruwa fiye da yadda kuke tunani!! Ina da wasu abokai waɗanda suka yi aure kwanannan suka gano cewa ashe yaya ne da ƙanwa
Kaleepha888 ya rubuta:
Wannan shiyasa a zamanin baya iyayen iyayen iyayen mu suke sanya su suyi gwajin jini kafin suyi aure. Ga dalilin nan.
Nupe_5 ya rubuta:
Ina nufin to a yanzu wane abu mutum zai iya yi? Ka riga da ka faɗa soyayya, ka santa ta sanka sannan ga yara! Ba wani abu da yayi saura da mutum zai yi.
Kinfi Sauran Mata: Magidanci Ya Fashe Da Kuka Lokacin Yayin Tuno Halaccin Da Matarsa Tayi Masa
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya fashe da kuka lokacin da ya tuno wani babban halaccin da matarsa tayi masa.
Wani matashi ɗan Najeriya ya fashe da kuka a wajen bikin murnar zagayowar ranar haihuwar matar sa.
Matashin ya fashe da kukan lokacin da take tuno halaccin da matar sa tayi masa lokacin da yake fama da talauci.