Wata budurwa mai yin aski ta karaɗe yanar gizo bayan bidiyon ta ya bayyana inda take yiwa wani aski da wuƙa.
Budurwar mai suna Lydia Williams ta sanya wani bidiyo a TikTok, wanda ya nuna yadda tayi amfani da wuƙar cikin ƙwarewa ta yiwa wani matashin yaro aski.
KU KARANTA KUMA: Sanata Uba Sani ya samu wani gagarumin tagomashi, wata babbar ƙungiya ta mara masa baya
A cikin bidiyon wanda yanzu haka sama da mutum dubu ɗari da hamsin suka kalle sa, yaron ya zauna yana jiran Lydia ta wasa wuƙarta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Masu bibiyar Lydia a manhajar TikTok sun yaba sosai lokacin da ta sanya wuƙar a kan matashin yaron, ta shige kamar wata reza mai kaifin gaske.
Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, Lydia ta kammala aske gashin kan yaron ba tare da tayi amfani da aska ba, inda tayi askin gabaɗaya da wuƙa.
Majiyar mu ta tattauna da Lydia inda ta bayyana cewa yin aski da wuƙa ya sanya ta zama ta daban da sauran masu aski.
Ku kalli bidiyon a nan
Bayan Mun Kwashe Dogon Lokaci Muna Soyayya, Saurayina Ya Auri Wata Daban -Budurwa Ta Koka
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta koka bayan saurayinta da suka daɗe suna soyayya ya auri wata daban bata sani ba.
Sa’o’i kaɗan bayan saurayinta ya kirata a waya, wata budurwa mai suna Anita Oghenero John, ta gano cewa ya auri wata budurwar daban.
Budurwar ta sanya hotunan su tare lokacin da suke shan ƙauna, yayin da take ta sharɓar kuka bayan yayi watsi da ita.