Kwamishinan Ilimi na Jahar Kano Muhammad Kiru, ya sanar da tsige Sabo Muhammad Ahmad shugaban Sakandire ta GSS Danbatta biyo bayan kin bin dokar da hukumar ta tanada bisa zuwa hutun babbar Sallah.
An sauke shine bisa kin tsayarda Daliban makarantar dake rubuta Jarabawar NECO dasu zauna a makarantar gaba daya lokacin har izuwa bayan Sallah.
Muhammad Kiru yace Ahmad Muhammad Sabo ya saki daliban ne sannan yayi tafiyarsa zuwa gidan kilan hutun Sallah ba tare da sanarma Ministiri na Ilimin ba.
KARANTA:- An kama wani mutum da zargin yi wa wata fyade a Dandalin Olympic na Tokyo
Yace an dauki wannan matakin ne saboda rashin bin doka da kuma cin amana da yayi. Kamar yadda Muhammad Kiru ya bayyana a jawabin sa.
Sannan Kiru ya umarci Ahmad Muhammad Sabo da ya halarta a Ministiri a ranar Litini.
Hukumar ta bada umarnin maye gurbin Ahmad Muhammad Sabo da wani nan take.
Idan baku manta ba gwamnatin Jahar Kano ta sanar da dukkan Dalibai dake rubuta Jarabawar NECO da su zauna a cikin Makarantu har sai an kammala Jarabawar, gwamnatin tace ta shirya musu abincin da za su ci, ciki harda shanu guda sha tara don shagalin Sallar Su. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Kamar yadda kwamishinan ya sanar gwamnatin ta shirya tsaf na daukar dawainiyar daliban har sai sun gama Jarabawar.
A wani labarin
Wani Minista ya sanyawa Limamai sharuda a lokacin babbar Sallah
Ministan babban birnin tarayya Abuja Muhammed Musa Bello, ya gindaya sharudda ga Limamai a lokacin gudanar da Sallah domin takaita yaduwar cutar Covid-19 karo na uku.
Wannan sanarwar ta fito ta hannun Sakataren sa Anthony Ogunleye.
Ministan ya sanya doka wajan gabatar da huduba kada tayi tsawo, sannan a kammala komi da komi a cikin awa daya.
Ya kara da cewa wajan gudanar da Sallah ya kasance an raba adadin masu shiga kashi biyu don samun tazara.
A yayin gabatar da bukukuwan Sallah a garin Abuja, yace duk wani gidan motsa jiki da na wasanni su kasance a kulle.
Duk a cikin bayanin nasa ya gargadi masu zuwa Sallah da su kasance sun sanya takunkumi suna bada tazara sannan da wanke hannu a koda yaushe.