Innocent Destiny wani dalibi ne mai kimanin shekaru ashirin da daya, wanda yayi yunkurin damfarar wani mutum a manhajar Wechat, inda dalibin yace masa shine Kim Webber, Kotu ta yanke masa hukuncin wankin bandaki har na tsawon kwanaki sittin. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Mai Shari’a Kezziah Ogbonnaya, ya umarci Jam’in gidan gyaran hali da ya samar ma Innocent Destiny rijistar da zai runka sanya hannu har na tsawon kwanaki sittin sannan a salllame shi.
Alkalin ya gargade Shi da ya zama dalibi mai bin doka, yace dashi idan kana fama da talauci ba shine zai sanya kazama Dan ta’adda ba.
KARANTA:- Da duminsa: Kotu ta hana yunkurin Cire Mataimakin Gwamnan Zamfara
Tun farko dai mai kare dalibin, ya roki kotu da ta yimasa adalci wajan hukunci, ganin dalibin yaro ne kuma wannan ne karo na farko da ya taba aikata laifi.
Kamar yadda Nuhu yace yaran yayi matukar nadama kan abunda ya aikata.
Dalibin ya tuba ya kuma yi alkwarin zai daina sannan zai watsar da dukkanin kayan aikin, Yana rokon anfuwar kotu sannan ya dau alkawari kan haka.
Ijeabalum Deribi lauyan Kotun, ta bukaci Destiny da lauya mai kareshi da su zo kotun su sanya hannu a ranar 22 ga watan July.
Deribi, ta so kotun ta yanke masa hukunci kamar yadda aka tanada na zaman gidan kaso na wata daya ko kuma tarar dubu dari.
Tace laifin ya keta dokar kundin kotun panel na shafi 332.
Comments 1