Ana wata ga wata, wani matashi da ake kira da suna Johannes Uli, ya dirkawa surikar sa ciki, ana tsaka da shagulgulan daura mashi aure da diyar matar mai suna Emmanuella Mathew, a wani gari da ake kira da suna ‘Kita’ a yammacin kasar Mali.
Wannan lamari ya faru ne, bayan da surikar ta nemi ya aure ta, amma ya nuna mata cewa shi diyar, ta tafi da imanin shi kuma ita yake son aure domin tafi dacewa dashi a zaman aure, a yayin da uwar tayi kunnen uwar shegu, tare da barazanar hana shi auren ta, gami da tura shi gaban kuliya.
Haka zalika, Ita dai surikar tuni ta fada a tarkon kaunar wannan kyakkyawan saurayi datake son hana diyar ta aure, inda ta bayyana cewa tuni kaunar shi ta shiga cikin zuciyar ta, don haka bazata iya hakuri ta barwa diyar ta auren shi ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Bata Bada Gaskiya Da Yaƙi Da Rashin Tsaro Ba – Akbishop, Alfred Martins
Surikar ta kasance bazawara tun bayan rabuwar ta da tsohon mijinta mai suna Mathew Okafor, inda ta cigaba da zama tare da ‘ya’yen ta, kasancewar ta mai hannu da shuni, sai ta cigaba da harkokin kasuwancin ta, ya zuwa lokacin da lamarin ya afku.
Yadda lamarin ya faru shine, a ranar 25 ga watan Disamba na shekarar 2020, Surikar mai suna Precious Mathew, ta fada tarkon kaunar Johannes bayan kawo mata shi da diyar tayi, a matsayin abokin ta na makaranta da suke karatu a tare, wanda surikar ta samu damar tattaunawa dashi a yayinda taje kawo mashi abinci.
Tunda ga wannan rana, Precious ta cigaba da gayyato wannan saurayi yana kwanciya da’ita har zuwa lokacin da ta samu ciki, wanda a cewar ta, tsantsar soyayyar datake mashi ne ya sanya harta bari tayi ciki dashi, domin ya zama tubalin cigaba da gudanar da rayuwar ta dashi, amma sai taga yana so ya yaudare ta, ta hanyar aurar mata d’iya.
KARANTA WANNAN LABARIN: DA DAMINSA: Shugaba Buhari Ya Cilla Zuwa Kasar Amurka
Precious tace bazata iya hakura da wannan saurayi ba, kasancewar ya kwanta da’ita kuma yana so ya yayi amfani da diyar ta, wanda ta bayyana a matsayin riba biyu kenan idan ta bari wannan lamari ya faru.
A dalilin haka ne ya sanya taje asibiti, kuma aka tabbatar mata dacewa tana dauke da cikin shi, shiyasa ta sanar dashi kuma ta bukaci ya janye maganar aure a tsakanin shi da diyarta, inda yayi kunnen uwar shegu da hakan, tare da cika bakin cewa taje ta dauki duk wani mataki data ke ganin zata iya.
Bayan ta sanar da d’iyar ta abunda ya faru, amma sai taki amincewa da janye maganar auren, tare da umartar ta, data nemo wanda yayi mata ciki, amma ba saurayin taba, domin koma shine babu abinda zai hana su shiga tubalin zama ma’aurata.
Anata bangaren, Emmanuella Mathew ta tabbatar dacewa tana yawan ganin shi yana zuwa gidan, amma ya ta’ba bayyana mata cewa, mamar su yake koyawa karatun sana’ar cinikayya ta zamani ta yanar gizo-crypto currency, wanda a lokacin da ta matsa mashi da tambaya, sai yace mata sun kusa kammala karatun.
Haka zalika, ta tabbatar dacewa biyo bayan wannan lamari na bakin ciki daya faru, a yanzu haka ta yanke shawarar rabuwa da saurayin ta, domin ya ci amanarta daya kwanta da mahaifiyar ta, wanda ko a lokacin da mahaifiyarta ta gaya mata, sai ta dauka da wasa take mata, kawai ta naso tayi amfani da talaucin da yake fama dashi, domin ta cimma muradinta na hana ta aure dashi.
A lokacin da Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta zanta da saurayin da lamarin ya faru dashi mai suna Johannes Uli,ya bayyana nadamar shi na kwantawa da mahaifiyar diyar da yake son aure, duk da ita ta tilasta mashi aikata hakan, domin ko a lokacin da ta nemi ya kwanta da’ita sai da ya hau dokin na’ki amma daga bisani ya biye mata.
Johannes Uli ya kara dacewa, surikar bata taba nuna mashi cewa tana son shi da aure ba, kuma bata taba nuna zata hana shi masoyiyar daya dade yana muradin aure a cikin zuciyar sa ba, sai yanzu data ga an kusa daura mashi aure sannan zata bullo da wani kauli da ba’adi.
Sai dai a cewar sa, shi yanzu bai shirya aurar tsohuwa sa’ar mahaifiyar sa, amma zai yi duk abinda zaiyi domin ganin ya juyo da hankalin wannan masoyiya tashi, domin tuni ya aza tubalin gudanar da rayuwa da’ita.
Jaridar Dimokuradiyya zata cigaba da bibiyar lamarin domin ganin ko za,a daura auren ko a kasin haka.