Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya amince da nadin mutum 180 a matsayi kari kan wadanda yake da su masu taimaka masa a matakai daban-daban, wanda ya hada da EA da STA.
Babban Sakataren gwamnan, Celement Nweke ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a garin Abakaliki, inda ya umurci dukkanin wadanda aka nada wanda ya hada tsoffin ‘yan majalisar jihar guda biyu, da su kawo takardunsu domin tabbatar da su.
Daga cikin wadanda aka nada sun hada da; Chidiebere Egwu, Igberi Nweme, Kelvin Opoke da Stephen Orogwu.
Sai kuma Maxwell Umahi, Dorathy Obasi, Oliver Nwachukwu, Cif John-Williams Nwode- Nnannna Nwangele da Nkem Madu.