Ana ci gaba da samun mabanbantar ra’ayoyi dangane da sakamakon Jarabawar Masu Sha’awar tsayawa takarar shugabancin Kananan Hukumomi da ya fito sa aka gudanar a Jihar Kaduna.
Mutane sama da dari ne dai suka Fafata a wannan jarabawa, wanda ke zama zakaran gwajin dafin zaben fidda gwani da za a yi a ranar biyar ga watan Mayun da muke ciki na shekara ta 2021.
Sakamakon zaben wanda aka fitar ranar Asabar da ta gabata ya nuna cewa mutane 75 daga cikin 115 da suka fafata ne dai suka samu nasara wadanda kuma za su fafata a zaben fidda gwanin.
Kazalika mutane 38 kuma sun fadi kasa warwas sakamakon rashin kuzari da suka nuna, lamarin da kenan ke nuni da cewa ba su babu batun shiga zaben fitar da gwanin.
Daya daga cikin su da ya gaza samun nasara, Muhammad Sani Abdulmajid ya ce gaskiya lamarin akwai rashin Kyautatawa a ciki duba da cewa ya samu maki 52.8, wasu kuma daga wasu kananan hukumomi da makin su bai kai haka ba an ce sun ci.
Kazalika Daraktan yaki neman zaben Kwamared Lawal Chanchangi wanda shi ma ya nuna sha’awar tsayawa takarar, ya ce an yi son kai tare da nuna karfin tuwo wajen zabar wadanda za su fafata zaben fitar da gwanin.
A hannu guda kuma ɗaya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya Ibrahim Isma’il daga karamar hukumar Kaduna ta kudu ya gode wa Sarki Allah bisa wannan nasara, inda ya ce bai ui mamakin wannan sakamako ba.