Wani dalibin fasaha dake kwalejin kimiyya da fasaha dake Kwara a Illorin mai suna Olawale, ya rugamu gidan gaskiya bayan da wasu Yan kungiyar asiri suka datse masa kansa. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
An ruwaito cewar Yan kungiyar asirin sun masa kwantan bauna ne bayan ya fito daga gida a ranar Talata.
An dai sami kansa ne a daidai sha tale-talen Unity dake Illorin bayan mahaifansa sun dade suna nemansa.
KARANTA:- Kulawa da dokar hanya bata hukumar FRSC kadai bane yana kan kowane mutum
Kawo yanzu dai ba’a ga ganagan jikinsa ba, har bayan tattara wannan rahotan.
Dalibin dai ya kasance yana gyaran waya ne a babbar Kasuwar waya dake Illorin.
Kamar yadda maman nasa ta bayyana tace “Yadai fita cikin gida a ranar Litini da misalin karfe 8, amma sai dai har lokacin dawowarsa tayi bai shigo ba, na kuma kira wayarsa amma gaba daya bata shiga.”
“Sai muka yanke shawarar mukai rahoto ofishin Yan sanda, bayan mun duba makarantarsu da Asibitoci bamu same shi ba.”
“Muna dai cikin nemansa ne sai muka ga mutane sunyi taro suna daukar hotuna, ashe suna daukar hoton kan yaran mune.”
A lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun Yan sanda, Ajayi Okasanmi, yace ana cigaba da bincike don kama wadanda sukai aika-aikar.
Bincike dai ya tabbatar da cewa Yan kungiyar asiri ne suka aikata wannan mummunan aikin.
“Shima dai dalibin ana zarginsa da shiga kungiyar asirin, dake kwalejin fasaha dake Kwara.”