Kwamishinan Ƴansandan mai barin gado na Jahar AIG Umar Muri, yace a karkashin jagorancin sa Yan sandan sunyi nasarar cafke mutane 492, sannan sunyi nasarar kwato shanu 679 tun daga daya ga watan January zuwa talatin ga watan July na wannan shekarar. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
A lokacin da suke gabatar da wasu Yan ta’adda da suka kama a ranar Juma’a, yace hukumar tayi nasarar kwace manyan Makamai irinsu AK47 guda sha tara, karamar bindiga kirar kasar waje guda biyu, manyan bindigu guda biyu, da sauran muggan makamai da akayi nasarar kwacewa a lokacin jagorancin AIG Umar Muri.
AIG Umar Muri, yace mutanen dai anyi nasarar cafke su ta fannin laifuka daban-daban, wadansu garkuwa da mutane, wadansu cin amana, wadandu infoma, wadansu masu satar shanu wadansu masu yin fyade, wadansu kuma an cafke su da laifin safarar miyagun kwayoyi.
KARANTA:- Rikicin Jam’iyya: Dan takarar shugabancin Jam’iyyar APC na Kano ya fadi
Ya cigaba da cewa masu lafi dari uku da sha biyar an damkasu zuwa ga kotu, inda mutane dari da saba’in da biyar sun fuskanci hukumci, sauran kuma ana cigaba da bincike a kan su.
AIG Umar Muri, wanda an maidashi zon 13, a Awka jahar Anambra, inda zai cigaba da kula da jahar Enugu da Anambra.
AIG Umar Muri, yace kasancewarsa a Jahar Kaduna yayi nasarori daban-daban wajan fada da muggan mutane.
AIG Muri yace “Hakika wannan ta’addanci ya janyo matsaloli ga rayuwar mutane gami da rusa tattalin arziqin kasar nan.”
“Abun bakin cikin ma shine ganin yadda yan ta’addan ke kara kaimi wajan aikata laifuka, duk da kokarin da Jami’an tsaro keyi don ganin sun dakile hakan.”
“A halin yanzu maganar da nakeyi da yawa daga cikin manoma basa iya zuwa gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda tsoron kasa ayi garkuwa dasu.”
“Kuma wannan zai kara sanya al’umma shiga matsalar abinci, wanda shima matsalar abinci yana gadar da rashin tsaro sosai a wannan kasar.”
“Duk da hakan hukumar mu na iya bakin kokarin ta wajan ta maida manoma su cigaba da aiki a gonakinsu, musamman ma wannan lokaci da muke nayin noma.”
“Idan har muka samu nasarar yin hakan, to tabbas zai taimaka wajan samar da tsaron a wannan jahar da ma wannan kasar baki daya.”
Comments 1