Wani abinda al’umma har yanzu ke mamakin aukuwar shi a birnin Landan da ya faru shine yadda aka ga dan wasan tsakiya na Tottenham Dele Ali da kuma yar gidan Kocin Manchester City Pep Guardiola mai Maria suna sunbatar juna a bainar jama’a.
Wani hoto da jaridar UK ta wallafa yadda Dele ya rungume wata budurwa wacce aka yi amannar cewa Maria ce ɗiya ga Guardiola.
Jaridar ta ruwaito cewa al’amarin ya faru ne a wani wurin shakatawa dake birnin na Landan.
Soyayyar tasu ta kullu ne bayan da Alli ya tunkare ta a yayin shagalin, inda suka kebe bayan doguwar zantawa tsakanin inda ta kai ga wannan al’amari.
Idan za a iya tunawa dai a yan baya-bayan nan ne Dele Alli da budurwarsa mai suna Ruby Mae suka rabu bayan dogon lokaci suna shan soyayya bisa abinda ta kira sharholiya da yake shafe talatainin dare yana yi.
Ko da yake a bangaren ta Maria ta ce babu komai a tsakanin ta da shi face abota ce mai karfi.