Tsohon magatakardan riko na hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire, Dakta Saleh Abubakar rasuwa.
A cewar wani makusancin marigayin, Alhaji Hassan Mijinyawa, wanda kuma shine mai baiwa gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba shawara kan harkokin yada labarai, Abubakar ya rasu ne a wani asibitin Kaduna bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Abubakar ya fito daga Jalingo babban birnin Taraba, amma yana zaune a Kaduna yana da shekaru 74 a duniya kafin rasuwar sa.
Tsohon magatakardan, wanda ya kammala karatun tarihi a shekarar 1973 a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya kuma kasance mamba a taron duba kan kundin tsarin mulkin Najeriya karkashin mulkin Manjo Janar Sani Abacha daga 1994 zuwa 1995.
A matsayinsa na Darakta a hukumar JAMB a shekarar 1996, Abubakar ya yi shekara 19 a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan ya kasance babban jami’in gudanarwa na kwalejin share fagen shiga jami’a a Yola a tsohuwar jihar Gongola.
Haka kuma ya jagoranci Kwalejin Ilimi ta Jalingo.
An binne gawar Abubakar a Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Kuma Ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya 12 da jikoki 11.