Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham dake ƙasar Birtaniya ta sanar da nada tsohon kocin Wolves Nuno Esperito Santo a matsayin sabon Kocin ta.
A watan Mayu ne Nuno ya yi bankwana da Wolves bayan shafe shekara huɗu yana jan ragamar Ƙungiyar.
Wannan nadi ya biyo bayan kai ruwa rana ne da Tottenham ɗin ta yi wajen ganin ta samu sabon koci bayan korar Jose Mourinho a watan Afirelu.
Da ma dai kuma kociyoyi da dama ne aka ruwaito cewa ka iya jan ragamar kungiyar ciki har da na Ajax Erik ten Hag da kuma na Leicester City Brendan Rodgers, sai dai yanzu haka lamarin ya sha ruwa.