Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta sanar da daukan Antonio Conte a matsayin sabon koci ta.
Hakan na zuwa ne sa’o’i 24 da sallamar Nuno Espirito Santo wanda a da ya rike mukamin a baya.
Sanarwar ta kara da cewa “Mun yi farin cikin sanar da nadin Antonio Conte a matsayin Babban Kocinmu kan kwantiragin har zuwa bazara na shekarar 2023, tare da zabin tsawaita kwantiragin,” kamar yadda Kungiyar ta fitar a s shafin yanar gizo.
Kafin nadin, Conte ya jagoranci Inter Milan zuwa gasar Serie A ta farko a kakar shekarar 2020/2021, wanda ya kawo karshen nasarar Juventus na lashe gasar har na tsawon shekaru 9 a jere.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sifeto Janar Zai Ziyarci Inda Gini Ya Rufta A Legas
Da yake magana bayan kulla yarjejeniya da kulob din, Conte ya ce, “Na yi matukar farin ciki da komawa aikin horarwa, kuma na yi hakan a kulob din Premier da ke da burin Inganta Nasarorinta.
A wani labarin Kuma na daban.
Jam’iyyar PRP za ta gudanar da taronta na kasa a ranar 11 ga Disamban shelarar, 2021.
Sakataren jam’iyar na kasa Alhaji Sule Kankara ne ya bayyana hakan a Katsina ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai.
Ya ce an kammala shirye-shiryen taron.
Ya kara da cewa jam’iyyar ta sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan matakin gudanar da babban taron.
Kankara ya kuma bayyana cewa a yanzu jam’iyyar PRP tana da sabbin shuwagabanni a jihar Katsina bayan taron da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.
A cewarsa, an gudanar da taron ne a garin Dandagoro dake karamar hukumar Batagarawa a jihar.
Ya Kuma ce an nemi ofisoshi goma sha daya a Majalisar zartarwar Jam’iyar a jihar, inda aka zabi Hassan Kankara a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na jiha.
Kazalika ya ce, An zabi Mallam Lawal Rimaye a matsayin sakataren jam’iyyar na jiha yayin da Aisha Lawal ta zama shugabar mata a jihar ta Katsina.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Farfesa Aliyu Jibiya daga Jami’ar Bayero, Kano; Alhaji Abdurrahman Abdallah, Malam Abu Yaradua, Alhaji Aliyu Tsauri da kuma Alhaji Musa Kankara.
Taron da jam’iyar ta gudanar ya Kuma samu halartar jami’an hukumar INEC a jihar da kuma jami’an hukumomin tsaro
Comments 2