Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham na shirin sayen Alvaro Morata don maye gurbin Harry Kane, dan wasan da ke kokarin raba gari da kungiyar a karshen wannan kaka bayan gaza cimma jituwar sayar da shi a kasuwar musayar ‘yan wasan da ta gabata.
Duk da cewa Kane bai samu damar komawa Manchester City a kakar da ta gabata ba, dan wasan ya tabbatar da cewa zai raba gari da Tottenham kafin karewar kwantiraginsa a shekarar 2022.
Shugaban Tottenham Fabio Paratici ya ce dan wasan mai shekaru 28 na jin dadin zamansa a kungiyar yanzu haka, duk da dambarwar da ta dabaibaye shirin sayar da shi a kasuwar musayar ‘yan wasan da ta gabata.
Sai dai sanarwar da Tottenham ta wallafa a shafinta ta ce tana fatan sayen Morata wanda yanzu haka ya ke taka leda da Juventus matsayin aro daga Atletico Madrid.
A baya-bayan nan ne Kane ya bukaci Tottenham ta yi gyara a kwantiraginsa don bashi damar iya raba gari da kungiyar gabanin karewar kwantiraginsa tare da kayyade kudin sakinsa kunshe a kwantiragin don saukaka cinikinsa.