Yunkurin Wasu masu Garkuwa da mutane ya gamu da cikas bayan da yan Bijilanti suka fatattake su da tsabar gudu lokacin da suka je niyyar sace mutane a yankin Kekeshi na karamar hukumar Abaji a birnin tarayya Abuja.
A yanzu haka dai wasu mutane huɗu da aka sace suna nan hannu madu garkuwa da su dina bayan da suka nemi fansar naira miliyan goma.
Wani mazaunin yankin wanda bai bukaci a bayyana sunan shi ba ya ce maharan sun zo ne a wuraren karfe tara da minti ashirin da biyu na almuru inda ya ce sun yi yunkurin kutsawa wasu gidaje toh amma hakar su ta gaza cimma ruwa.
Ya Kara da cewa wani dan Bijilanti dake aiki a yankin shi ya lura da hasken tocila da bai aminta da shi ba yayin da yaje zagawa.
“Wani dan bijilanti ne dake zama a yankin ya zaga don yin fitsari bayan wani gida, to sai ya ga hasken tocila daga nesa nan da nan sai shi ma ya haska nashi” A cewar mazaunin Kekeshi.
Kazalika ya bayyana cewa bayana ganin haka sai ɗaya daga maharan ya harba Bindiga a iska, ba kuma tare da wata-wata ba yan Bijilanti din suka maida wuta.
Daga bisani ya ce karar bindigar yan bijilantin ne ya sa maharan suka ranta a na kare.