By Ishaq Dabai
Farashin litar man fetur yayi tashin gwauron zabi a yau Talata a wasu sassa na jihar Anambara biyo bayan samun sabani tsakanin direbobi masu dakon man fetur PTD da kuma gwamnatin jihar Anambara data IMO.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an samu bam bamcin farashin man fetur a Awka, da babban birnin jihar da Onitsha da kuma Nnewi inda ake sayar da man fetur akan naira 165 kafin tashin sa kawo yanzu ana sayar dashi akan naira 175,zuwa 180 da kuma 200 akan kowacce lita.
Karin farashin man fetur ya sanya karuwar kudin tafiye tafiye a sassan jihar inda ya sanya mutane kokawa da tsadar inji wani direba mai suna Mr Uche Obasi.
A cewar wani mai saida man fetur a karamar hukumar Orumba ta Arewa Chief Okey Enekwe ya bukaci gwamnatin jihar da tasa baki akan al’amarin saboda a cewar sa man fetur a Anambara ya ragu biyo bayan yajin aikin da masu dakon man fetur PTD keyi a yankin.
Kungiyar dillan man fetur ta najeriya IPMAN reshen jihar Anambaracikin wata sanarwar data fitar tace ta bukaci gwamnatin jihar Imo data warware rashin jituwar dake tsakanin su da direbobi masu dakon man fetur cikin gaggawa kamar sauran sassan kasar nan.
Shugaban kungiyar IPMAN reshen jihar Anambara, Ebonyi Da kuma jihar Enugu cikin wata sanarwar data fitar mai dauke da sa hannun shugaban ta Mr Chinedu Anyaso da kuma sakataren kungiyar Mr Emeka Iloafor sunce rikicin zaiyi tasiri a Jihar kogi da Benue da Cross River duba da cewa ma’ajiyar su daya idan suka bar dakon man fetur.
“Suna rokon gwamnoni jihohi kudancin kasar nan dasu sa baki kamar yadda yake faruwa a daya daga cikin membar mu ta jihar Imo, kungiyar PTD ta dakatar da samar da man fetur a jihohin kudu maso gabas a daya gefen kuma kungiyar IPMAN ta rufe wuraren kasuwanci su a Jihar Imo.wannan shawarar da membobin kungiyar suka bayar ta jawo karancin man fetur”, a cewar sanarwar.