Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya tuhumi wasu tsaffin Gwamnoni da Gwamnoni masu ci da ƙoƙarin kawo ɓaraka cikin Jam’iyyar.
Adamu ya bayyana hakan ne a jawabin bude taron majalisar zartaswar jam’iyyar APC, NEC, dake gudana a Transcorp Hotel Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan bindiga Sun Saki Matar Kwamishinan Filato, Ɗiyar ta
Shugaba Muhammadu Buhari; Mataimakinsa Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar Dattawa da na Wakilai, Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila, duk sun halarci Zaɓen.
Adamu ya ce duk da cewa Gwamnoni ne jagororin jam’iyya a jihohinsu, ya kamata ru rika Girmama tsaffin Gwamnonin jihar. Saboda a baya sune shugabanni kuma wajibi akwai mabiyansu da ba zasu do su ga an ci mutuncisu ba