Kwamitin tsaftar muhalli na ƙarshen wata-wata da gwamnatin Kano ta kafa ya cafke ɗan wasan kwaikwayon nan Mustapha Musty wanda aka fi sani da Naburaska.
An cafke ɗan wasan ne a unguwar Tudunwada dake ƙaramar hukumar Nassarawa bisa karya dokar zama a gida domin tsaftar muhalli har zuwa ƙarfe 10 na safe.
Mustapha Naburaska a tattaunawarsa da gidan rediyon Freedom yace ya fito ne domin zuwa jana’iza cikin rashin sani, amma yanzu ya fahimci cewa tsaftar muhalli ta kore kowanne uzri.
A ƙarshe kotun tafi da gidanka ƙarƙashin mai shari’a Auwal Yusuf Sulaiman ta ci tararsa naira dubu biyar, amma daga bisani ya nemi afuwa tare da nuna nadamarsa, a don haka kotu ta yi masa sassauci ya biya naira dubu uku.