Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano ta ce shirye shirye sun kammala domin ganin an gudanar da tsaftar muhalli ta karshen wata da aka saba gudanar da ita a duka ranar asabar din karshen wata.
Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Ismail Garba Gwammaja ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai, yana bukatar alumma da su bayar da hadin kai wajen zama a gida tare da tsaftace muhallansu, daga karfe 7 zuwa 10 na safe.
KARANTA ANAN: Kungiyar ASUU Ta Maka FG A Kotun Daukaka Kara
Ya kara da cewa sun tanadi jami’an tsaro a wannan karon kamar yadda aka saba, domin rangadi tare da tabbatar da kowa yabi dokar, da kuma hukunta wadanda suka bujire mata.
A nasa bangaren kwamishinan kula da muhalli na jihar Kano Dr Kabiru Ibrahim Getso ya ce tuni an tanadi kotunan tafi da gidanka, wadanda zasu hukunta duk wanda aka samu da laifin karyar dokar tsaftar muhallin ta gobe Asabar.
A wani labarin kuma: Ambaliya: Mazauna Suna Cikin Hadari, Yayin Da Kogin Benue Ya Kai Wani Mataki.
Mazauna yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Benue sun bar gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa.
Kwamishinan Muhalli da albarkatun ruwa Dokta Godwin Oyiwona, ya shaida wa jaridar Daily trust a ranar Juma’ar nan cewa, ambaliyar ruwan ta haura zuwa mita 11.1 a kan matsalar ambaliyar ruwa a kogin Benue.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Oyiwona ya kara da cewa, a shekarar 2012, kogin ya mamaye gabarsa a lokacin da matakin ya kai mita 12, kuma hakan ya kori mazauna yankin da dama.