Ƙasar Afghanistan na fuskantar barazanar rashin bada tallafin jin ƙai a ƙarƙashin mulkin Taliban, a yayinda iyaye tuni suka fara sayar da ƴaƴan su domin samun kuɗin da zasu ciyar da kansu.
Wannan na zuwa ne ƴan watanni kaɗan bayan Taliban ta karbe ikon ƙasar, biyo bayan cire sojojin Amurka daga Ƙasar.
Wakiliyar BBC Yogita Limaye ta tattauna da wata uwa data saida ɗiyar ta akan kuɗi Dala $500 domin ta samu kuɗin da zata cida sauran ƴaƴen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Ikpeazu ya rantsar da Kwamishinoni 27
Kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyya ta bayyana, mai sayen wanda ba’a ambaci sunan sa ba, kuma ba’a tabbatar da manufar shi ba, yace yana son ya raini yarinyar domin ya aurawa ɗan shi.
“Ya bada Dala $250, wanda sun isa ciyar da iyalai na ƴan watanni kaɗan, kuma zai biya sauran idan ya dawo karɓar yarinyar idan ta fara tafiya,” inyi matar.
“Sauran ƴaƴana suna mutuwa a dalilin yunwa, to dole in Saida ɗiyata. Ta yaya bazan ji babu daɗi ba, ɗiyata ce, naso ace ban saida ɗiyata ba.”
Wani uba wanda baya samun kuɗi, yace dole sai sayar da ƴaƴan su domin basu da zaɓin daya wuce haka.
“Muna matuƙar fama da yunwa. A halin yanzu bamu da filawa, babu mai a gida, bamu da komai. Ɗiyata bata san makomar ta a rayuwa ba. Bansan ta yaya zata ji ba, amma dole in Saida ta.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta gano cewa kimanin yara 8 aka bada rahoton mutuwar su har lahira sakamakon fama da yunwa a babban birnin Ƙabul na Afghanistan a wannan satin.
Wani mai goge-goge a yammacin Ƙasar Afghanistan mai suna Saleha, ya sayar da ɗiyar shi mai shekaru 3 ga wani mutum dake binshi bashin Dala $550.
“Idan rayuwa ta cigaba da wakana a wannan ƙangin talauci, to zan kashe ƴaƴe na da kaina,”Saleha ya shaida, inda yace yanzu bai san mi zai ci a daren ba.”
“Zanyi ƙoƙari in samo kuɗi domin kare rayuwar ɗiyata,”. Inji magidanci Abdul Wahab.
Khalid Ahmad Mai bada bashi, ya shaida cewa dole ya karɓi ɗiyar mai shekaru 3 domin ya dai-dai ta bashin, domin cewar sa bashi da kuɗi kuma basu biyashi abinda yake bin su ba,” inji shi.