Daga Sabiu Musa Kano
Kwamishinan ‘Yan sanda na jahar Enugu ya bada umarni ga bangaren binciken manyan laifuka da su binciki lamarin.
Mai magana da yawun ‘Yan Sandan jahar ta Enugu SP Ebere Amariazu, yace kwamishinan ya ba da umarnin binciken ne ga Jami’an da suka kama matar mai shekaru 30 inda ake Zarginta da halaka ‘Yar ta mai watanni 17 da Haihuwa.
Majiyar mu ta rawaito mana cewa matar mai suna Ijeoma Naji, ta kashe ‘Yar mai suna Chiemerie Naji ranar Alhamis 30 ga watan mayu na 2019, ba tare da sanin dalilin aikata hakan ba.
Kamar yadda mai magana da yawun ‘Yan sanda yace kwamishina Balarabe Sulaiman ya bada umarni kan yin binkicen kwakwaf domin Gano Dalilin da yasa Matar ta aikata wannan Aika-aika ga ‘Yar Cikin ta.