bagudu

Tsaro: An Jinjinawa Gwamna Bagudu Na Kebbi

Jam’iyyar PRP a jihar Kebbi ta jinjinawa gwamnan jihar, Atiku Bagudu bisa wanzar da zaman lafiya a kafatanin jihar.

Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Alkali Galadima shi ne ya yi wannan jinjinar a taron jam’iyyar da ya gudanar a ranar Alhamis a Birnin Kebbi.

A cewarsa, jihar tana daya daga cikin jihohi wadanda suke zaune lafiya a fadin kasarnan musamman idan aka yi duba da karancin laifuka da ake aikatawa a jihar.

Alhaji Alkali Galadima ya ce su a jam’iyyarsu ta PRP suna jinjinawa gwamna Bagudu da sauran masu ruwa da tsaki musamman Sarakuna bisa yadda zaman lafiya ya wanzu a jihar.

Ya ce a lokacin da sauran jihohi suke fama da ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama’a, amma jihar tana ci gaba da zaune lafiya cikin yardarm Allah da kuma matakan da gwamnati ke dauka wajen tabbatar da zaman lafiyar.SHARE.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *