Kasar Birtaniya ta ce mai yiwuwa mayakan Boko Haram su kara azama wajen yin garkuwa da ‘yan kasashen waje, abinda ya sa ta gargadin’ yan kasarta kan yin balaguro zuwa wasu jihohi goma sha biyu a Najeriya.
Ofishin kula da Harkokin Wajen Birtaniya, ne ya fitar da wannan sanarwa tun a makon da ya gabata wadda ke kunshe cikin shawarwarin da ya baiwa ‘yan kasar dangane da jadawalin tafiye-tafiye a Najeriya.
Gwamnatin kasar ta Birtaniya ta ce akwai babbar barazanar garkuwa da mutane a duk fadin Najeriya, bisa dalilai na siyasa, kudi ko kuma tsattsauran ra’ayin addini ko akida, tare da yin hasashen cewa, barazanar za ta fi shafar ‘yan kasashen waje da kuma ma’aikatan agaji.
Jihohin da ke tattare da matsalar rashin tsaron dai sun hada da Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Kaduna, Katsina, da kuma Zamfara a arewacin Najeriya, yayin da kuma a Kudanci suka hada da Delta, Bayelsa da Rivers da Akwa Ibom, sai kuma Cross River.
Gwamnatin Birtaniya ta kuma shawarci ‘yan kasar da su yi taka-tsantsan saboda abubuwan da ka iya biyo bayan bikin cika shekara daya na zanga -zangar #EndSARS musamman a Legas da Abuja.