Gwamnatin jihar Kaduna ta nemi ‘yan banga da su hada kai da jami’an tsaro a kodayaushe wajen yin ayyukansu nay au da kullum.
Gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufa’i ne ya yi kiran nan a lokacin da yake kaddamar da ofishin ‘yan bangan a Doka karkashin jagorancin Kanar Usman Dudu mai ritaya.
El-Rufa’i, wanda Kwamishinan harkoki da tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya wakila, ya jaddada kokarin gwamnatin na fada da ta’addanci a jihar.
A cewarshi, gwamnatin jihar Kaduna ba za ta bar ‘yan bangan su dauki doka a hannunsu ba ta hanyar rike wadanda suke zargi. Ya bukacesu da su mika wa ‘yan sanda duk wani wanda ake zargi da aikata laifi.
“Wani abu mai muhimmanci shi ne, ko sanar da jami’an tsaro sun komai kuma ka kasance masu bin doka akan aiki,”inji shi.
A nashi jawabin, Shugaban ‘yan bangan, Alhaji Shehu Dantudu ya ce samar da ‘yan bangan zai taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci.
Ya ce tsaro yana da muhimmanci a rayuwarmu saboda idan babu tsaro babu ci gaba.
Sannan ya nemi Kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya taimaka musu wajen horas da ‘yan bangan, saboda a cewarshi “tare zamu rage ta’addanci a cikin al’umma.”
Daga karshe, Shugaban Kungiyar bunkasa Doka, KADDA, Alhaji Nuhu Isa ya jinjina wa gwamnatin jihar, ya kuma bukaci gwamnatin ta taimaka musu da motoci don saukin aikin.