Tsaro: Kogi NSCDC ta horas da Jami’an ta akan yadda zasu yi aiki da Makaman su
Hukumar Jami’an tsaro ta Sibil Difens ta horar da Ma’aikatan ta akan yadda zasu riƙe makamai a Kogi.
Kwamanda-Janar na Hukumar NSCDC Dr. Ahmed Audi ya bayyana cewar, wannan lamarin nada manufr maido da Ƙarfin Hukumar zuwa turba mai kyau.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba zamu fasa yin babban taro a ranar 26 ga Maris — Martanin APC ga INEC
Ya bayyana haka a ranar Juma’a a lokacin da yake jawabi a bikin yaye Jami’an a horaswar da suka samu akan yadda zasu kula da Makaman su a makarantar Horaswar ta Lokoja, yana mai ƙara dacewa horasda Ma’aikatan ya zama wani yunƙuri na inganta ƙwarews da sanin Makamar aiki. Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya bayyana.
Da ya samu wakilcin Daraktan Shari’a Umar Mohammed, Audi yayi kira ga Jami’an dasu tabbatar da ƙwarewa a lokacin da suke gudanar da aikin su.
Tunda Farko Kwamandan NSCDC a Kogi, Suleiman Mafara ya taya su murna da kammala ɗaukar horon, yana mai cewa nasarorin da aka samu a samamen da suke kaiwa, baza’a same su ba, in babu goyon bayan Kwamanda-Janar.