Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana rahoton da mujallar labarai ta ‘The Economist dake birnin London ta wallafa akan kasar, a matsayin cin zarafi da kuma bata sunan gwamnati da gangan gami da yunkurin haifar da rudani.
Labarin da gwamnatin Najeriya ke raddi kansa, mai taken, ‘Fagen aikata laifuka a Zuciyar Afirka’, ya bayyana cikin mujallar ta ‘The Economist’ ne a ranar Asabar 23 ga watan Oktoba.
Mujallar ta bayyana gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wadda ta rasa madafa zalika gaza magance matsalar cin hanci da rashawa.
Har ila yau, ta zargi sojojin Najeriya, wadanda ta bayyana a matsayin “masu karfi kan takarda,” da sayar da makamai ga masu tayar da kayar bayan dake tagayyar al’ummar kasar.
Sai dai cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, daraktan hulda da jama’a na rundunar sojan Najeriya, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana labarin a matsayin makarkashiyar masu son zubar da darajarsu a idon duniya ta hanyar shafa musu bakin fenti.