Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tare babbar hanyar Birnin Gwari/Funtua, sun kashe wani direba tare da yin garkuwa da matafiya da dama.
Daily Post ta rawaito cewa Wani mazaunin yankin, Alhaji Ibrahim Yusuf ne ya tabbatar da hakan a yammacin ranar Litinin din nan.
Ya kara da cewa lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Satumba, 2022. Shi ma da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban kungiyar masu fafutukar ganin ci gaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Usman Kasai a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce biyo bayan farmakin da sojoji suka kai a kan babbar hanyar Birnin Gwari/Kaduna, a yanzu ‘yan bindiga sun karkata akalar su zuwa babbar hanyar Birnin Gwari/Funtua.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun kai farmaki kan masu ababen hawa, inda suka yi garkuwa da wasu har ma da kashe wasu daga cikin wadanda abin ya shafa.
Ya ce a halin yanzu, babu wata mota da take bin hanyar a sakamakon toshewar da aka yi a baya-bayan nan.
KARANTA ANAN: Sowore Ya Bayyana Yadda Ya Taimaki Peter Obi Wajen Samun Takara A LP
Ya ce sojojin sun bi ta Kaduna zuwa hanyar Birnin-Gwari da Birnin-Gwari zuwa Funtuwa, inda aka samu wasu nasarori da suka hada da kawar da wasu ‘yan bindiga da aka kama a wasu al’ummomi da ke kewaye da hanyoyin, inda ya kara da cewa wannan kokari abin yabawa ne domin suna godiya kwarai da gaske.
Sannan ya yabawa gwamnati da sojojin Najeriya bisa wannan nasara da kuma sabon yunkuri na yaki da rashin tsaro a yankin.
Sanarwar ta bayyana jin dadin kungiyar da kasancewar jami’an tsaro da aka girke a kewayen titin Kaduna zuwa Birnin-Gwari, inda ta ce wannan matakin ya rage musu hankali matuka, domin a yanzu sun dauki matakin a matsayin wani yunkuri na magance hare-haren da ake ci gaba da kaiwa a hanyar Birnin-Gwari/Kaduna.
A wani labarin kuma: Harin Gidan Yarin Kuje: Ministan Buhari Ya Amince Da Gazawar Jami’an Tsaro
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya amince da cewa jami’an tsaro sun kasa dakile harin da ‘yan ta’adda suka kai a cibiyar gyaran hali ta Kuje da ke Abuja.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 5 ga watan Yuli, 2022, a daidai lokacin da ake kokarin samar da kayan aiki ga jami’an.