By Abbas Yakubu Yaura
Wani jami’in hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) Abdulkareem Ojonla Jimoh ya gamu da ajalinsa a lokacin da yake bakin aiki a hanyar Sagamu-Ore zuwa birnin Benin.
An ce yana halartar wani da ake zargi da laifin cin hanci da rashawa a wata mota kirar Toyota Previa mai lamba SMK-687GG lokacin da wani direban wata farar motar Toyota Hiace mai lamba NEM-618AA ya afka masa.
Sanarwar da kwamandan FRSC ya fitar a kan babbar hanyar, Lasisi Ogundele, ya ce direban motar ya rasa yadda zai tafiyar da motarsa sakamakon birki da ya yi masa gardama da kuma kokarin kaucewa karo da wasu motocin da ke kan layi a shingen binciken da aka yi wa Abdulkareem.
Sauran motocin da abin ya shafa a cewar sanarwar, sun hada da wadanda ake zargi da laifin safarar ababen hawa, wata mota kirar Toyota Picnic mai lamba GKB-367XA da kuma Opel Zafira mai lamba AAB-293AM.
Kazalika Sanarwar taci gaba da cewa Abdulkareem ya samu munanan raunuka kuma ya mutu yayin da aka garzaya da shi zuwa asibiti dan samun kulawar likitoci.
Sai dai kuma yayin da wanda ake zargi da laifin safarar motoci wanda shi ma ya samu munanan raunuka ya mutu jim kadan bayan an garzaya da shi babban asibitin Ore a karamar hukumar Odigbo.
Ya ce an ajiye gawarwakin mutanen biyu a dakin ajiye gawa na Opeyemi, Ore yayin da aka kai karar ga ‘yan sandan Araromi.