By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane shida ne na cocin Deeper Life Bible da ke unguwar Iragbo a Badagry a jihar Legas, suka samu munanan raunuka a ranar Lahadin da ta gabata, a lokacin da ginin Cocin ya ruguje a yayin da ake ci gaba da gudanar da ibada.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya biyo baya ta kai ga rugujewar ginin Cocin da misalin karfe 9:30 na safe.
Daya daga cikin mabiya Cocin wanda shi ma abin ya shafa, Topohozin Tunde, ya shaida wa NAN cewa mabiya Cocin su shida sun samu munanan raunuka.
“Ni ma na samu mummunan rauni a gwiwa, amma alhamdulillahi ba a samu asarar rai ba.
“Da misalin karfe 9:30 na safiyar ranar Lahadi, yayin da ake gudanar da ibadar, an yi wata guguwa mai karfi wadda ta afkawa ginin cocin, kuma kafin mu iya sanin abin da ke faruwa, ginin cocin ya ruguje.
“Wasu sun iya tserewa, yayin da mu kusan shida muka samu munanan raunuka,” in ji shi.
Mista Tunde ya ce an ba su kulawar lafiya, amma ba a ba su kulawar da ta dace ba saboda babu likita a asibitin.
“Wadanda suka samu munanan raunuka an kai su babban asibitin Badagry domin samun kulawar da ta dace.
“Tunda rauni na bai da yawa, na yanke shawarar kula da kaina,” in ji shi.
Shi ma da yake magana, Thoma Agodi, Baale na kabilar Iragbo, ya ce yana cikin fadar sa ne wani mazaunin garin ya zo ya shaida masa cewa ginin cocin ya rufta.
“Dole ne mu gode wa Allah da ba a samu asarar rai ba sakamakon rugujewar,” in ji shi.
NAN