Tsawa mai karfin gaske ta yi ajalin wasu jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) har mutum uku a jihar Ogun.
Kakakin hukumar a jihar ta Ogun, Florence Okpe ce ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ibtila’in ya rutsa da su ne a daidai lokacin da suke tsaka da aikinsu a ranar Laraba a yankin tsohuwar tollgate da ke karamar hukumar Ijebu-North East.
Inda ta yi karin haske da cewa; “lamarin ya auku ne a lokacin da jami’an ke cikin ofishinsu a daidai lokacin da suke shirin fitowa fareti da misalin karfe 10 na safe.” Inji ta.