Gwamnatin tarayya ta ce za ta gana da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) a kotun masana’antu ta kasa (NICN) a ranar Litinin domin yanke hukunci kan tsawaita yajin aikin.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Dakta Chris Ngige, Ministan Kwadago da tabbatar da nagartar aiki ne ya bayyana haka ranar Lahadin nan a Abuja a wata wasika da ya aikewa magatakardar NCN, mai kwanan watan 8 ga watan Satumba.
Ngige ya bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ‘yan jaridu da hulda da jama’a, Olajide Oshundun a ma’aikatar kuma ya rabawa manema labarai.
Ya ce zaman tantancewar ta zama dole ne biyo bayan gazawar tattaunawa tsakanin kungiyar da ma’aikatar ilimi ta tarayya.
Karanta kuma: Wata Kotu Ta Gayyaci Kungiyar ASUU Kan Tsawaitar Yajin Aiki
Ya kara da cewa za a gabatar da maganar da karfe 9 na safiyar ranar 12 ga watan Satumba.
“Gwamnatin tarayya ta bukaci hukumar ta NICN ta binciki halaccin yajin aikin da shugabannin kungiyar ASUU da mambobin kungiyar suka dade suna ci gaba da yi.
“Ta bukaci kotu da ta fassara gabadayan tanadin sashe na 18 LFN na shekarar 2004, musamman yadda ya shafi dakatar da yajin aikin da zarar ministan kwadago da samar da ayyukan yi nema tare da sasantawa,” inji shi.
Ya kuma ce hukumar ta NICN za ta fassara sashe na 43 na dokar rigingimun kasuwanci, Cap T8. LFN 2004, mai taken “Tallafi na Musamman tare da mutunta biyan albashi yayin yajin aiki da kulle”.
Ngige ya ce hakan “musamman mu’amala da hakkokin ma’aikata a lokacin duk wani yajin aiki ko kulle.
“Shin ASUU ko wata kungiyar da ta tsunduma yajin aikin na iya neman a biya su albashi ko akwai bayanan tanadin doka.
“Kayyade ko ‘yan kungiyar ASUU sun cancanci a ba su alawus-alawus ko ‘yajin aiki’ a lokacin da suke yajin aiki, wanda ya fara a ranar 14 ga watan Fabrairu.
“Morarsu, bisa la’akari da dokar mu ta kasa kamar yadda aka tanada a sashe na 43 na TDA da ka’idojin aiki na kasa da kasa kan ‘yancin yajin aiki da kuma shawarar kwamitin ILO kan ‘yancin kungiyoyi a kan batun,” in ji shi. (NAN)
A wani labarin kuma: Ma’aikatan Jiragen Sama Sun Tsayar Da Aiki A Filin Jirgin Saman Kano
Ma’aikatan filin jirgin sama sun kawo cikas a harkokin zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin Mallam Aminu Kano (MAKIA) sakamakon takaddamar da ta kunno kai tsakanin hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya FAAN da hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya NAMA.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa jiragen da zasu tashi daga Kano a safiyar yau litinin sun samu cikas yayin da jami’an kula da zirga-zirgar jiragen suka dakatar da ayyukansu wanda ya shafi sauka da tashin jirage.