Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa bai kamata a tunzura shugaban kasa Buhari wajen daukar matakin tsige manyan hafsoshin tsaro ba, saboda shi kadai ya san inda matsalar take.
Buratai ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar TheCable, Thisday da kuma gidan talabijin na Arise a ranar Talata, 11 ga watan Fabarairu a jahar Legas.
Idan ba ku manta ba, a kwanakin baya majalisar dokokin Nijeriya ta nemi Buhari ya sallami kafatanin hafsoshin tsaron Nijeriya saboda abin da suka bayyana a matsayin gazawarsu wajen kare rayukan ‘yan Nijeriya, duba da sake farfadowar da Boko Haram ta yi.