Kungiyar goyon bayan Tinubu, TSO sun taya gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq da sauran iyalai ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa.
Babban Daraktan kungiyar, Ibrahim Dahiru Danfulani shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar ta’aziyyar da ya fitar a madadin kungiyar ta su.
Sanusi Muhammad Burdugau, wanda shi ne jami’in yada labaran kungiyar, shi ne ya raba takardar ga ‘yan jarida a Abuja a ranar Asabar, inda suka bayyana Marigayi Abdulganiyu a matsayin wani jigo wajen ci gaban kasarnan musamman a bangaren shari’a, wanda suka ce ya cancanci a yi koyi da shi.
Danfulani har wala yau ya mika ta’aziyyarsa ga al’ummar jihar Kwara baki daya, da kuma gwamnatin Kwara bisa wannan rashi.
A karshe sun yi addu’ar Allah ya jikan Marigayin, yasa aljanna makoma.