Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi kira da a kara wa’adin da babban bankin Kasa CBN ya sanya domin daina amfani tsofaffin takardun kudin Naira da ke yawo.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa babban bankin Kasa ya bayar da ranar 31 ga watan Junairu, 2023 a matsayin wa’adin daina amfani tsofaffin takardun kudin Naira yana mai dagewa cewa ba gudu ba ja da baya kan wa’adin.
‘Yan Najeriya da dama dai sun yi ta kiraye-kirayen CBN da ya kara wa’adin ya duba yadda ake fama da karancin kudi na Naira da kuma matsalar kin amincewa da tsofaffin takardun Naira wajen yin ciniki.
KU KARANTA KUMA Martani Atiku Bayan Rashin Nasarar Adeleke A Gaban Kotu
Atiku a cikin wani faifan bidiyo na minti biyu da dakika talatin da biyar da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Abdulrasheed Uba Sharada ya fitar a ranar Asabar din nan ya ce wa’adin yana haifar da kunci ga jama’a.
A cewar Atiku, sake fasalin kudin ya zama ruwan dare gama gari a fadin duniya, don haka halin da ake ciki a Najeriya ba sabon abu bane sai dai wa’adin ranar 31 ga watan Janairu yana haifar da kunci ga jama’a.
‘’Yawancin ‘yan Najeriya musamman manoma da masu sana’ar hannu da kuma wadanda ke yankunan karkara ba su da asusun ajiyar banki, don haka ba za a kai ga lokacin sauya tsofaffin takardun kudi zuwa sababbi ba, “in ji Atiku a cikin bidiyon.
Ya kuma yi kira da a kara wa’adin domin a magance halin kuncin da jama’a ke ciki.
A Wani Labarin Kuma Hukumar NBTE Ya Tabbatar Da Fadada Shashin Koyar Aikin Jarida A Kwalejin Fasaha
Hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE) ta tabbatar da bullo da fadada ilimin koyan aikin jarida zuwa sassa 3 daban-daban da kuma shirin aiwatar da irin wannan a cikin karatun kimiyyar kwamfiyuta.
Sakataren zartarwa na hukumar Farfesa Idris Mohammed Bugaje ne ya bayyana hakan a Kaduna a wajen rufe taron kwana biyar na sabbin manhajojin da manyan masu ruwa da tsaki suka yi a ranar Juma’a.