Babban Bankin Najeriya CBN ya fayyace matsayinsa game da daina zama doka kan tsofaffin takardun kudi na N1,000, N500, da N200 bayan wa’adin ajiye takardun kudin da abin ya shafa a ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023.
Da yake magana da manema labarai a Abuja, a ranar Talata, Daraktan sashen sadarwa na CBN, Mista Osita Nwanisobi, ya bayyana cewa tsofaffin takardun za su daina zama doka bayan 10 ga watan Fabrairu, 2023, kuma ba za a iya amfani da su ta kowace hanya ba na ciniki bayan haka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanusi Ya Zama Abin Koyi, Buhari Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Sarkin Dutse
Sai dai ya bayyana cewa a bisa tanadin sashe na 20(3) na dokar CBN, ‘yan Najeriya za su samu damar karbar darajar Naira ne kawai a babban bankin kasar, bayan da kudin ya rasa matsayinsa na kasuwanci dangane da cika wasu sharudda.
Da yake nanata alkawarin da Gwamnan Babban Bankin na CBN, Godwin Emefiele ya yi a taron Majalisar Wakilai a ranar Talata, Nwanisobi ya ce ‘yan Najeriya ba za su yi asarar kudadensu ba, duk da cewa ya bukaci ‘yan kasar da su yi amfani da damar da aka tsawaita wa’adin na ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023 don saka tsofaffin takardun kuɗin da ke hannunsu a bankunan su ko ta hanyar wakilan kuɗin wayar hannu.
Da yake ambaton wasu lokuta a wasu yanayi, Nwanisobi ya yi bayanin cewa takardun kudin Naira da suka daina zama doka, hukumomin kuɗi na irin waɗannan hukunce-hukuncen ne kawai za a iya fansa da su bisa ga sharuɗɗan / tsari kamar yadda Babban Bankin ya tsara.
Nwanisobi ya kuma yi amfani da wannan damar wajen karfafa wa ‘yan Najeriya kwarin gwiwar yin amfani da wasu hanyoyin biyan kudi domin mu’amalarsu, yana mai cewa tsarin biyan kudin Najeriya yana da karfi sosai kuma yana cikin na farko a duniya.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Isa Abuja Daga Jihar Jigawa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a yammacin ranar Talata, ya isa fadar shugaban kasa ta Villa dake Abuja, daga ziyarar aiki da ya kai jihohin Legas, Katsina, Kano da Jigawa.
Jirgin saman Leonardo AW139 mai saukar ungulu daya dauko shugaba Buhari daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe ya isa Aso Rock Villa mintuna kadan bayan karfe 7:00 na dare.