Tsoffin sojoji da suka yi ritara sun nemi gwamnatin tarayya da ta kafa musu hukuma mai dauke da tsoffin sojoji a karkashin ma’aikatar tsaro ta kasa domin lura da walwalarsu.
Tsoffin Sojojin sun yi wannan kiran ne a wata takarda da suka rabawa manema labarai a ranar Asabar a birnin tarayya Abuja a karshen taron da suka gudanar mai taken ; “Unification of Military Veterans Associations”. Wato Kungiyar gamayyar tsoffin sojoji.’
Sannan sun tabbatar da cewa za su yi aiki ne a karkashin kungiyarsu ta “Veterans Federation of Nigeria.” Sun yi alkawarin bai wa gwamnati hadin kai, inda suka ce a shirye suke da su ba da gudummawa wajen tabbatar da tsaro a kasarnan, inda kuma suka yi kira ga hukumar tsaro ta kasa, da hedikwatar tsaron da su bunkasa bayanansu a hukumar.