Tsoho Ɗan Shekaru 62 ya Faɗa Cikin Wata Ƙatuwar Rijiya a Kwara
An tsinto gawar wani Tsoho Mai Shekaru 62 Mai suna Ibrahim Tajudeen daga wata rijiya daya faɗa a Ilori, Jahar Kwara.
An gano cewa lamarin ya faru ne bayan Asibitin Olayemi kan hanyar Jirgin Sama na yankin Gbagba, Ilori da misalin ƙarfe 8:00 a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƙuri’ar Jin Ra’ayin Kafa Ƙasar Biafra: Kotu ta sake ɗage Shari’ar zuwa 20 ga Oktoba
Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa a ranar Asabar, Marigayin ya Kasance yana fama da matsalar taɓin hankali kafin faruwar lamarin.
“Muna zaune a waje, sai muka ga mutum ya tafi kai tsaye zuwa Rijiya. Babu wanda ya taɓa tunanin zai faɗa a cikin Rijiyar.
“A lokacin da muka je muna duba wa ashe tuni ya faɗa a cikin Rijiyar”, kamar yadda majiya ta bayyana.
Mai Magana da Yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jahar Kwara Hassan Adekunle ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Mun miƙa shi ga Onawole Najeem babban yayan sa, wanda ya tabbatar da cewa Shekarun sa 62.
“Daraktan Hukumar Kashe Gobara na Jahar Kwara Prince Falade John Olumuyiwa ya bayyana rashin jindaɗi akan faruwar lamarin, sai ya shawarci Al’umma dasu zama masu haƙuri da Maƙwabtan su domin magance sake faruwar lamarin”, Inji Hassan.