:Rundunar Yan sanda ta tabatar da kama wani magidanci mai suna, Bayo Akinwete, mai shekarau 65, kuma har ma ta mika shi a gaban wata Kotun Majestri dake Jihar Ado Ekiti, bayan data kama shi da laifi yima Yar cikin sa mai shekaru biyar Fyade dumu dumu.
Dan sanda mai kula da laifin Insfekta Monica Ikebuilo, ta bayyanawa Kotun cewar mahaifin Yarinyar Akinwete, ya yiwa Yariyar Fyade ne a ranar 18, ga watan Yuni 2019, a Unguwar Olorunsogo dake cikin babban birnin jihar Ekiti, Ado Ekiti.
Yar karamar Yarinyar ta bayyana mana cewar Baban nata ya dade yana kwakular ta; inji Yan sanda.
Yariyar tace da ita da Yayar ta mai kimanin shekaru 9 suna zaune da Baban su bayana da Mahaifiyar su ta tafi ta bar su kan cewa baza ta zauna da mahaifin su ba.
Tace ya dade yana Bani Gaban shi yana cewa in yi wasa da shi ko kuma yace in dunga shafa mishi ita, wata rana ma ya tilasta mun na sha giya karshe na gan shi a kai na ya danne ni bayan na farfado, shine sai na gayawa makocin mu abun da Babana yake mun shine ya kawo ni wajen Yan sanda.
Yanzu haka dai Kotun tana kan bincike kuma ta sha alwashin hukunta shi.