By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin rusasshiyar jam’iyyar SDP, kuma shugaban majalisar koli ta shari’a a Najeriya SCSN, Dakta Ibrahim Datti Ahmed, ya rasu a kano.
Dattijon wanda ya kasance daya daga cikin manyan likitocin Kano na farko da aka rawaito ya rasu ne da sanyin safiyar Alhamis yana da shekaru 83 bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Idan za’a iya tunawa cewa fitaccen likitan a shekarar 2013 ya ki yin aiki a kwamitin da shugaba Goodluck Jonathan ya kafa domin sasantawa da ‘yan Boko Haram .
Dakta Datti Ahmed a wancan lokaci mai muhimmanci ya zargi gwamnatin tarayya da “rashin gaskiya” kan yadda take magance tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Gabas.
Likitan ya bar mata daya da ‘ya’ya 10, kuma tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.