By Ishaq Dabai
Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya yi kira ga al’ummar Nigeria, cewa su yi karatun ta nutsu kan ‘yan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023, tare da zaben na gari daga cikin su.
Tsohon Gwamnan na wannan kalami ne yayin wani gangamin siyasa da nufin ziyara, wanda wasu mambobin jam’iyyar PDP suka shirya tare da kaiwa Sule Lamidon a gidansa dake Bamaina, a karamar hukumar Birnin Kudu.
Wannan martanin nasa na zuwa ne dai dai lokacin da al’umma ke kiraye Kirayen cewa, ya kamata ya fito takarar shugaban kasa a 2023.
Dangane da masu wannan kiran ne Tsohon gwamnan ya ce kamata yayi ace al’umma su sake dubawa cikin manyan yan siyasa, maimakon kira gare shi, shi daya kwal da cewa ya cancanta, yana mai tabbatar da cewa idan suka sake dubawa, tabbas, za a samu wanda ya fi shi cancanta.
Amma duk da hakan shugaban jam’iyyar PDP a jihar Jigawa Dr Ibrahim Babandi, ya tabbatarwa da Sule Lamido cewa dole ne shima yabi sahu wajen tsayawa takara a zaɓen dake tafe na 2023.