Yanzu dai za a iya cewa ta faru ta kare wai an yi wa mai zani ɗaya sata, domin tsohon Gwamnan Jihar Imo Chief Ikedi Ohakim ya koma jam’iyyar APC.
Ohakim wanda daya daga yan gani kashe-nin tsohon gwamnan jihar Emeka Ihedioha ya sanar da sauya shekarsa ne a ranar Laraba a garinsa na Okohia dake karamar hukumar Isiala Mbano.
Mista Ohakim ya dare kujerar gwamnan Imo ne a shekarar 2007 a karkashin inuwar jam’iyyar PPA kafin daga bisani ya koma PDP.
Ko da yake tun a farko sune ma’asassa jam’iyyar PDP a shekara ta 1999, amma daga bisani ya koma PPA ne a 2006 inda ya tsaya takara kumabya samu nasara.
Tsohon Gwamnan ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya bada gudummawarsa a ɗaga daraja APC a jihar da ma kasa baki daya.