Akwai alamomin da ke nuna cewa wadanda suka mutu a jihar Bauchi a zamanin Gwamna M.A sun sami gata mai yawan gaske. Domin kuwa sabon Gwamna Bala Kauran Bauchi ya ce MA ya kashe sama da naira Biliyan biyu wajen sayen likkafani da sauran kayan yiwa gawa sutura.
Wani abu ma shi ne, tsohon Gwamnan ya ragargaji wadannan kudade ne ýan watannin kalilan kafin a tuntsurar da shi daga kan kujerar Gwamna a karo na biyu.