- Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai wa tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ziyarar ban girma a gidansa da ke Minna, jihar Neja.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito cewa mai taimakawa tsohon gwamna Saifullahi Hassan kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Asabar.
Hassan bai bayyana makasudin ziyarar da kuma abin da shugabannin biyu suka tattauna ba.
Babu tabbas ko ziyarar tana da nasaba da babban taron jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso yamma ko kuma muradin Kwankwaso a shekarar 2023 mai zuwa.