By Ishaq Dabai
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Monday Igbuya da tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, Cif Hon Edoja, sun bar jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.
Shugaban jam’iyar PDP na Delta, Mista Kingsley Esiso, a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar, Latimore Oghenesivbe ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa ana shirin babban taron PDP da za a yi a filin wasa na Sapele Township a ranar 23 ga watan Oktoba, don maraba dasu.
Sanarwar ta bayyana cewa ana sa ran gwamnan jihar Delta, Dakta Ifeanyi Okowa, zai karbi wadanda suka sauya sheka zuwa PDP a taron.
A cewar sanarwar, Shugaban na Delta ta tsakiya na PDP, Cif F. Fovie da membobin zartarwarsa na tsakiya tare da ofishin shugaban jam’iyyar na jihar tuni sun kammala shirye -shiryen mayar da taron siyasa abin tunawa.
Har ila yau, Esiso ya lura cewa babban taron gangamin yana daya daga cikin jerin shirye-shiryen da aka shirya don nuna fifikon siyasa na PDP a matsayin ita kadai ce ke da kyakkyawar alakar siyasa da mutanen kirki na jihar Delta, gabanin babban zaben 2023.