Tsohon shugaban majalisar dattawa, Joseph Wayas ya rasu a wani asibiti a birnin Landan.
Har kawo hada wannan rohoton dai ba’asami Cikakkun bayanai game da mutuwarsa ba.
Wayas yana da shekaru 80 a duniya ya shugabanci majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu.
Gwamna Ben Ayade na Cross Rivers ya yi alhinin rashin Wayas, dan asalin jihar.
A wata sanarwa da Christian Ita, mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, ya fitar a madadinsa, Ayade ya bayyana mutuwar a matsayin wani babban rashi.
“A matsayinmu na Yan jihar Corss Rivers Mu na cikin bakin ciki yayin da muke alhinin rasuwar fitaccen dan mu. Ya kasance mai daraja. Rasuwar Dr Wayas hakika babban rashi ne ga jiharmu da Najeriya Baki daya.”
“A matsayinsa na Shugaban Majalisar Dattawa, Dr Wayas ya ba da gudummawar zurfafa tsarin dimokuradiyyar Najeriya ta hanyar kwazonsa da yayi wajan shugabancin majalisar dattawan kasar nan”
“Kuma tun daga lokacin da tsohon shugaban majalisar dattawan ya yi ritaya daga harkokin siyasa, yana taka rawar uba da daidaita al’amura a cikin harkokin siyasa da al’amuran jiharmu,” in ji sanarwar.
Ga iyalan marigayin, Ayade ya ce, “Muna tare da ku a cikin wannan lokaci na bakin ciki. Muna Kuma tare da ku a cikin zukatanmu da addu’o’inmu.”