Villarreal ta nada tsohon kocin Arsenal Unai Emery a matsayin sabon kocin kungiyar a inda ya kulla yarjejeniyar shekaru uku.
Emery dan kasar Sipaniya mai shekaru 48, ya maye gurbin Javi Calleja ne wanda ya bar kungiyar duk da cewa ta karkare a matsayin ta biyar a kan tebur.
Bayanai sun nuna cewa Emery ya bar Arsenal ne a watan Nuwambar bara.
Kuma dama a can baya ya jagoranci Sevilla da Valencia da kuma kungiyar PSG ta Faransa.
Emery shi ne kuma wanda ya maye gurbin Arsene Wenger a watan Mayun 2018 bayan ya lashe gasar Europa sau uku a jere tare da Sevilla da kuma lashe gasar kwallon kasar Faransa tare da PSG.