Tsohon kocin Barcelona Ronald Koeman, ya caccaki tsarin kocin kungiyar Xavi na raba yan wasa zuwa mataki na 4-3-3 a Camp Nou, yana mai cewa Barcelona ta rayu a baya.
Koeman ya kuma yi tsokaci kan zawarcin da Barcelona take yi, inda zata iya siyan Robert Lewandowski na Bayern Munich a wannan bazarar.
Kocin dan kasar Holland wanda Barcelona ta sallame shi a watan Oktoban da ya gabata sakamakon rashin samun sakamako mai kyau da kuma zargin rashin amfani da sanannen tsarin kungiyar na tiki-taka, ya shaidawa Esport3 cewa: “Na yarda da mamaye wasan.
“Barca tana rayuwa a baya, daga 4-3-3, daga ‘tiki-taka’. Kwallon kafa ya canza. Yanzu ba za ku iya rayuwa kamar a baya ba.”
Ya kara da cewa, Lewandowski babban dan wasa ne, mai yawan zura kwallo a raga, amma ya kai wasu shekaru masu yawa a rayuwar sa.
“Zan yi shakku da yawa game da sanya hannu a kansa ko kuma ba zan saye shi ba.” In ji Shi.