Tsohon kwamishinan ayyukan jihar Kano wanda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tube sakamakon ‘yin murna’ da mutuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar, Abba Kyari, ya ce ya kamu da cutar korona.
A waki sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, Injiniya Mu’azu Magaji, ya ce yanzu haka yana cibiyar killace masu dauke da cutar korona a ke Kano. Inda tsohon Kwamishinan ya nemi da al’umma su taya shi da addu’a.
A watan jiya ne Injiniya Mu’azu Magaji ya janyo ce-ce-ku-ce bayan kalaman da ya yi wasu kuma suke ganin kamar na nuna murna ne da rasuwar Abba Kyari, wanda ya mutu sakamakon kamuwa da cutar korona.
Sai dai kwamishinan — wanda bai musanta cewa ba shi ya wallafa bayanan ba — ya nuna nadama a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce rashin fahimtar bayanan da ya wallafa a Facebook aka yi, har ta kai ga daukar matakin tube shi daga mukaminsa na kwamishina.