Tsohon kwamishinan harkokin waje na jihar Imo, Fabian Ihekweme, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, wato PDP.
Ihekweme ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC, zuwa PDP tare da wasu mambobin jam’iyya mai mulki ne a yau Laraba.
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu da Sakataren jam’iyyar, Sanata Samdaddy Anyanwu ne suka tarbi wadanda suka sauya shekar a filin wasa na Kanu Nwankwo da ke Owerri dake jihar.
Haka kuma an karbe shi a hukumance ga jam’iyyar PDP har da wani babban mai ruwa da tsaki, shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Charles Ezekwem.
Ezekwem ta yi watsi da PDP zuwa APC a shekarun baya kafin ya sawa a yau laraba.
Ya koma PDP ne tare da daruruwan magoya bayansa.
A wani labarin Kuma na daban.
An kashe masu kada kuri’a yayin da ‘yan bindiga suka kai hari a rumfunan zabe a Enugu
Kimanin mutane biyar ne ake fargabar sun mutu a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a rumfunan zabe biyu a yayin zaben kananan hukumomi a jihar Enugu, ranar Laraba.
Yan bindigar sun mamaye rumfunan zabe da ke Obeagu ward III a karamar hukumar Enugu ta Kudu da kuma wata rumfar zabe da ke Akpugo a karamar hukumar Nkanu ta Yamma.
Masu dauke da makamai sun tarwatsa dandazon Jama’a ne ta hanyar lalata kayayyakin zabe bayan sun fatattaki masu kada kuri’a.
Baya ga wadanda aka kashe, wasu sun samu raunuka yayin da aka kona motoci da dama.
Wani ganau da bai so a ambaci sunansa ba, ya ce an ji ’yan bindigar suna kururuwa cewa sun yi gargadin cewa kada a sake yin zabe a wani yanki na Kudu maso Gabas.
Da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sanda a Enugu, Daniel Ndukwe, ya shaida wa wakilin Jaridar Daily Trust cewa ya sake kiransa saboda yana cikin aiki.