Tsohon mai horas da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Enyimaba International dake garin Aba da Rangers International dake jahar Enugu wato Gbenga Ogunbote ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sunshine Stars na garin Akure.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Sunshine Stars ce ta sanar da hakan a shafinta na twitter a wannan rana ta Talata inda tace ta sayeshi ne domin yin gyara na yadda zasu sake saka azama musamman a gasar ajin Firimiya ta ƙasar nan.
Ogunbote dai gogaggen mai horas wane inda ya san yadda gasar ajin Firimiya take ciki da bai sannan muma ya kan yi ƙoƙari sosai a duk ƙungiyar ƙwallon ƙafan dayaje a matsayinsa na mai horas wa.
Haka zalika mahukunta ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Sunshine Stars sun bayyana cewar suna buƙatar ƙungiyar ta fara wakiltar ƙasar nan a gasar zkarun nahiyar Afrika kokuma gasar ajin ƙwararru ta nahiyar Afrika inda hakan shine burinsu.
A yanzu dai ana daf da sanya ranar daza a fara fafata gasar ajin Firimiya ta ƙasar nan wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 inda tuni wasu ƙasashen sun fara fafata wasannin masu musamman a nan nahiyar Afrika dama duniya baki ɗaya.